Yanda za'ayi amfani da kwayoyi

Akwai magunguna kala biyu da ake amfani da su domin zubar-da-ciki: mifepristone da kuma misoprostol Cubar-da-ciki da kwayoyi yana aiki sosai idan har duka waɗannan magungunan an yi amfani da su. Har wa yau, idan ba a samu mifepristone ba, to misoprostol ma shi kaɗai zai yi aiki domin kawar da ciki kuma hakan shi ma bashi da wata matsala.

Zaɓi in kina son ki sami sani dangane da sharuɗa na zubar-da-ciki cikin sauƙi tare da mifepristone da kuma misoprostol ko kuma misoprostol shi kaɗai.

Cikinki yana cikin satin 13 na farko (kwanaki 91)
Kin karanta dukkan
How to Use

Sharuɗan Domin Amfani Da Kwayoyin Zubar-Da-Ciki Na Mifepristone da kuma Misoprostol

Kafin farawa, fara karanta shawarwarinmu a kai Kafin Yin Amfani Da Kwayoyin. Ki tabbatar:

Sharuɗan Domin Amfani Da Kwayoyin Zubar-Da-Ciki Na Mifepristone da kuma Misoprostol

Domin zubar-da-ciki da kwayoyin mifepristone da kuma na misoprostol, kina da buƙatar ki sha kwaya ɗaya 200mg da kuma huɗu zuwa takwas 200mcg na kwayar mifepristone. Kuma kina da buƙatar kwayar kashe raɗaɗi a tare da ke, kamar ibuprofen, domin ya taimaka wajen sarrafa zafin. Acetaminophen da paracetamol ba sa aiki a kan raɗaɗi yayin zubar-da-ciki saboda haka ba a yarje musu ba.

Ga yadda ake amfani da mifepristone da misoprostol a tare domin kawar da juna-biyu:

Mataki na 1:

Haɗiyi kwaya ɗaya 200mg ta mifepristone tare da ruwa.

Mataki na 2:

Jira zuwa awa 24-48.

Mataki na 3:

Sanya kwayar misoprostol guda huɗu (200 mcg ko wacce) a kan harshenki ki ajiyesu a nan tsawon mintuna 30 yayin da suke narkewa. Ba zaki yi magana ko cin wani abu ba a tsawon wannan mintuna 30, saboda haka yana da kyau ki samu wurin da yake ba hayaniya inda ba za a dameki ba. Bayan mintuna 30, sai ki sha ruwa sannan ki haɗiye duk abinda yayi saura na kwayar. Sannan wannan shine lokacin da ya dace ki sha maganin kashe raɗaɗi kamar ibuprofen, domin murɗa zata fara nan da nan.

Zaki fara zubar da jini da kuma murɗeɗeniya a cikin awanni 3 na amfani da kwayar misoprostol guda huɗu.

Mataki na 4:

Bayan awa 24 da shan kwayoyi huɗu na misoprostol, idan baki fara zubar da jini ba, ko baki da tabbacin cikin ya zube, sanya wasu kwayoyin huɗu na misoprostol a kan harshenki. Ajiyesu tsawon mintuna 30 yayin da suke narkewa. Bayan mintuna 30, sai ki sha ruwa sannan ki haɗiye duk abinda yayi saura na kwayar.

Sauran abin lura dangane da zubar-da-ciki tare da Mifepristone da kuma Misoprostol:

Ki san me kuma za a jira aukuwarsa bayan shan mifepristone da kuma misoprostol a nan.

Idan kin fuskanci mummunar murɗawa, to kwayar ibuprofen kyakkyawan magani ne domin magance raɗaɗi. Zaki iya sayan ibuprofen kimanin 200 mg a wurin saida magani (ba tare da takardar izinin likita ba)a ƙasashe da dama. Sha kwaya 3-4 (200 mg ko wanne) a duk awanni 6-8. Idan kina buƙatar ƙarin abin kashe raɗaɗi, zaki iya nan ma amfani da kwaya guda 2 na Tylenol (325 mg) duk awanni 6-8.

Idan kin damu da hanyar zubar-da-ciki sannan kina buƙatar ƙarin taimako, zaki iya saduwa da abokai a www.safe2choose.orgwww.womenhelp.org or www.womenonweb.org.

Idan kin yi amfani d kwayoyin zubar-da-ciki na mifepristone da misoprostol, kuma ta yiwu bakya son zuwa cibiyar kula da lafiya domin ziyarar bincikawa. Waɗannan magungunan suna da aminci sosai har ma Hukumar Lafiya ta Duniya ta yarje cewa kina da buƙatar ziyarar bincikawar ne kaɗai idan:

 • Kina jin rashin lafiya, ko kuma ciwonki baya yin sauƙi bayan kwanaki 2 ko 3. Idan wannan ta auku, yi sauri ki nemi tallafin masana lafiya.
 • Har yanzu kina ƙara jin alamun juna-biyu sati biyu bayan kin sha kwayoyin zubar-da-ciki.
 • Zubar da jininki yana zuwa da karfi kuma bai yi sauƙi ba bayan sati 2.

Sharuɗan Zubar-Da-Ciki Tare Da Misoprostol Kaɗai

Kafin farawa, fara karanta shawarwarinmu a kai Kafin Yin Amfani Da Kwayoyin. Ki tabbatar:

Idan mifepristone baya samuwa a inda kike, zaki iya amfani da misoprostol shi kaɗai domin kawar da ciki.

Domin zubar-da-ciki da misoprostol kaɗai, kina da buƙatar shan kwayoyi guda goma sha biyu 200mcg na misoprostol. Kuma kina buƙatar samun kwayoyin kashe raɗaɗi a tare da ke, kamar ibuprofen, domin sarrafa raɗaɗin. Acetaminophen da paracetamol ba sa aiki a kan raɗaɗi yayin zubar-da-ciki saboda haka ba a yarje musu ba.

Ga yadda ake amfani da misoprostol shi kaɗai domin kawar da juna-biyu:

Mataki na 1:

Sanya kwayar misoprostol guda huɗu (200 mcg ko wacce) a kan harshenki ki ajiyesu a nan tsawon mintuna 30 yayin da suke narkewa. Ba zaki yi magana ko cin wani abu ba a tsawon wannan mintuna 30, saboda haka yana da kyau ki samu wurin da yake ba hayaniya inda ba za a dameki ba. Bayan mintuna 30, sai ki sha ruwa sannan ki haɗiye duk abinda yayi saura na kwayar. Sannan wannan shine lokacin da ya dace ki sha maganin kashe raɗaɗi kamar ibuprofen, domin murɗa zata fara nan da nan.

Mataki na 2:

Jira tsawon awa 3.

Mataki na 3:

Sake sanya wasu kwayoyin misoprostol guda huɗu (200 mcg) a kan harshenki ki ajiyesu a nan tsawon mintuna 30 har sai sun narke.

Mataki na 4:

Jira tsawon wasu awannin 3.

Mataki na 5:

Sake sanya wasu kwayoyin misoprostol guda huɗu (200 mcg) a kan harshenki ki ajiyesu a nan tsawon mintuna 30 har sai sun narke.

Zaki fara zubar da jini da murɗeɗeniya yayin shan kwayoyin. Ki tabbata kin shanye duka kwayoyi 12 ɗin ko da kin fara zubar da jini kafin ki gama shanyesu.

Sauran abin lura dangane da zubar-da-ciki tare da Misoprostol:

Ki san me kuma za a jira aukuwarsa bayan shan misoprostol a nan.

Idan kin fuskanci mummunar murɗawa, to kwayar ibuprofen kyakkyawan magani ne domin magance raɗaɗi. Zaki iya sayan ibuprofen kimanin 200 mg a wurin saida magani (ba tare da takardar izinin likita ba)a ƙasashe da dama. Sha kwaya 3-4 (200 mg ko wanne) a duk awanni 6-8. Idan kina buƙatar ƙarin abin kashe raɗaɗi, zaki iya nan ma amfani da kwaya guda 2 na Tylenol (325 mg) duk awanni 6-8.

Idan kin damu da hanyar zubar-da-ciki sannan kina buƙatar ƙarin taimako, zaki iya saduwa da abokai a www.safe2choose.orgwww.womenhelp.org or www.womenonweb.org.

Idan kin yi amfani da misoprostol, kusan ba ki da buƙatar ziyartar cibiyar kula da lafiya domin ziyarar bincikawa. Waɗannan magungunan suna da aminci sosai har ma Hukumar Lafiya ta Duniya ta yarje cewa kina da buƙatar ziyarar bincikawar ne kaɗai idan:

 • Kina jin rashin lafiya, ko kuma ciwonki baya yin sauƙi bayan kwanaki 2 ko 3. Idan wannan ta auku, yi sauri ki nemi tallafin masana lafiya.
 • Har yanzu kina ƙara jin alamun juna-biyu sati biyu bayan kin sha kwayoyin zubar-da-ciki.
 • Zubar da jininki yana zuwa da karfi kuma bai yi sauƙi ba bayan sati 2.

Marubucin:

 • Dukar bayani da an samu alaman tsa a wanan yanar gizo ne an rubuta daga hannu kungiyar HowToUseAbortionPill.org yarda aka samu a cikin misali daga National Abortion Federation, Ipas, Hukumar Lafiya Ta Duniya (World Health Organization), DKT kasa da kasa (International) dakuma carafem.
 • National Abortion Federation (NAF) ne sanaa kungiya wande ke bada zubar da ciki a arewa amirka, da shugaba daya a cikin zabi motsi. Bayani akai HowToUseAbortionPill.org ne aka hada da 2020 Jagororin Manufofin Asibiti (Clinical Policy Guidelines) Wanda NAF ya saki.
 • Ipas kawai ne kungiya kasa da kasa wande yeke fadada anfani zubar da ciki wanda ba a bata ba da kuma kula da kwakwalwa. Bayani akai HowToUseAbortionPill.org ne aka hada da Sabunta Asibiti acikin Lafiyar Haihuwa 2019 Wanda Ipas ya saki.
 • Hukumar Lafiya Ta Duniya (The World Health Organization) ne musamman hukumar na Gama Duniya (United Nations) da yake alhakin lafiyar jama’a na kasa da kasa. Bayani akai HowToUseAbortionPill.org ne aka hada da 2012 zubar da ciki wanda ba a bata ba: jagorancin fasaha da siyasa na tsarin lafiya Wanda WHO ta saki.
 • DKT kasa da kasa kasa da kasa ne kungiya da an rejista, wanda ba ta riba ba, da haka kafa a 1989 domin ta kula da ikon kasuwancin jama’a a wasu babban kasashe wanda sukada bukatun mai girma na tsarin iyali, HIV/AIDS rigakafin dakuma zubar da ciki wanda ba a bata ba.
 • carafem ne cibiyar sadarwa asibiti wande ke baya da dace da sanaa akulawa da zubar da ciki da tsarin iyali domin mutane su lura da lamba dakuma tazarar yaran su.

Nassoshi:

HowToUseAbortionPill.org na da alaka da kungiya mai zaman kanta wanda ke da rajista a kasar Amurka 501c(3)
HowToUseAbortionPill.org na bada bayani don wayarwa ne kadai, kuma bata da alaka da wani kungiyar lafiya

Ɗaukar nauyi daga Women First Digital